2 Yuli 2021 - 18:14
Najeriya : Kotu Ta Sanya Ranar 28 Ga Watan Yuli, Domin Yanke Hukunci Kan Shari’ar Sheihk Zakzaky

Babbar kotun jihar Kaduna a Najeriya, ta sanya ranar 28 ga Yuli don yanke hukunci kan shari’ar da ake wa Sheihk Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeenat.

ABNA24 : A zaman na ranar Alhamis, dukkan lauyoyin masu gabatar da kara da wadanda ake kara sun yi wa kotu bayani.

Babban lauya ga Malam El-Zakzaky, Femi Falana, wanda ya yi magana da manema labarai jim kadan bayan dage zaman, ya roki Kotun da ta yanke hukunci a kan wadanda yake karewa.

Tun a shekara ta 2015 ne dai ake tsare da malamin, da maidakinsa bayan farmakin Zariya.

342/